'Za mu mayar da dajin Sambisa wurin atisayenmu'

Sojojin Nigeria na sauke tutar Boko Haram

Asalin hoton, Nigerian Army

Bayanan hoto,

Dajin dai na da fadin murabba'in kilomita dubu sittin.

Hukumomin soji a Nigeria sun ce za su mayar da dajin Sambisa - inda ya kasance sansanin mayakan Boko Haram tun shekara ta 2013 - wurin atisaye.

A makon jiya ne dai shugaban kasar, Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cewa sojojin sun yi nasarar kwace dajin daga hannun mayakan.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasa Birgediya-Janar Sani Usman Kukasheka ya shaida wa BBC cewa za a yi hakan ne domin tabbatar da cewa ''wasu miyagun mutane ba su fake a wannan dajin ba.''

Janar Kukasheka ya ce kuma nan gaba kadan za su yi wa 'yan kasar bayanin abubuwan suka tarar a dajin bayan fattatakar mayakan Boko Haram daga sansanoninsu.