Shugaban Romania ya ki aminta da nada musulma mukamin farayin minista

Sevil Shhaideh in Bucharest (21 May 2015) Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Jam'iyyar PSD ce ta bayar da sunan Sevil Shhaideh bayan nasarar da ta samu a zabe

Shugaban kasar Romania Klaus Iohannis ya ki amincewa ya nada wata mata musulma wadda jam'iyyar masu ra'ayin sauyi ta PSD ta ba shi sunanta domin nada ta mukamin farayin minista.

Da an amince da nadin nata da Sevil Shhaideh za ta kasance mace kuma musulma ta farko da ta zama farayin minista a kasar.

Shugaba Iohannis dai bai fadi dalilin kin amincewa da nadinta ba, amma dai ana sukar Ms Shhaideh da rashin gogewa a siyasa saboda sau daya ne kawai ta taba rika mukamin minista.

Masu sharhi kan al'amurran siyasa a kasar sun ce hakan bai rasa nasaba da kasancewar mijinta dan kasar Syria.

A martanin da ya mayar shugaban jam'iyyar ta PSD Liviu Dragnea ya ce jam'iyyarsa za ta iya duba yiwuwar tsige Mr Iohannis.

Ya ce babu wata hujja a kundin tsarin mulkin kasar ta kin amincewa da ita, kuma ya zargi shugaban da son tayar da wani rikicin siyasa a kasar.

Karin bayani