Colombia ta amince da yi wa 'yan tawayen Farc afuwa

Jerin gwano mayakan kungiyar Farc

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An kiyasta cewa kungiyar ta Farc na da mayaka 20,000 lokacin da take kan ganiyarta.

Majalisar Dokokin Colombia ta amince da wata doka da ke tayin afuwa ga wasu da ake zargi da aikata kananan laifukka yayin yakin basasar da aka kwashe shekaru ana yi.

Shugaba Juan Manuel Santos ya yaba da kafa dokar a zaman matakin farko na kara karfafa zaman lafiya da 'yan tawayen na kungiyar Farc.

Shirin afuwar wani bangare ne na yarjejeniyar zaman lafiyar da aka yi wa gyaran fuska; bayan da 'yan kasar suka ki amincewa da yarjejeniya ta ainihi a cikin wata kuri'ar-raba-gardama.

Fadan dai ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 260,000 kuma ya raba miliyoyi da gidajensu.