Tauraruwar Hollywood Debbie Reynolds ta rasu

Debbie Reynolds (a hannun hagu) da 'yarta Carrie Fisher

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Debbie Reynolds (a hannun hagu) da 'yarta Carrie Fisher

Tauraruwar fina finan Hollywood Debbie Reynolds ta rasu kwana daya bayan mutuwar 'yarta Carrie Fisher wacce itama tana harkar fim din a Amurka.

Ta rasu tana da shekara tamanin da hudu.

Dan marigayiyar ya ce mahaifiyarsa ta yi matukar kaduwa da mutuwar 'yar uwarsa Carrie.

An gaggauta garzayawa da Debbie Reynolds zuwa asibiti ne bayan ta samu matsalar shanyewar bangaren jiki a gidan danta Todd Fisher da ke Beverly Hills, lokacin da suke tattauna yadda za a tsara jana'izar Carrie Fisher.