An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria

Yakin Syria

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shekaru 5 kenan ana yaki a Syria

Gwamnatin Syria da 'yan tawaye sun amince da a tsagaita wuta a duk fadin kasar, sakamon tattaunawar sulhun da aka yi.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ne ya sanar da haka, ya yin da ministan harkokin wajen Turkiyya ya tabbatar da shirin yin hakan.

Kasashen Rasha da Turkiyya da ke marawa bangarorin da ke yaki da juna baya, su ne za su kasance wakilan su.

Turkiyya ta ce cikin yarjejeniyar da aka cimma har da dakatar da bude wuta ta sama, sai dai wasu daga cikin mayakan jihadi na IS ba su shiga tattaunawar ba.

A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar free Syrian army, ta ce kungiyar IS da Nusra Front wadda ta juye zuwa Jabhat Fateh al-Sham da sauran kungiyoyin da ke mara musu baya sun kauracewa tattaunawar.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani dan tawaye na cewa babu yankunan da mayakan IS ke fakewa a cikin yarjejeniyar.