Zan jefo barayin gwamnati daga jirgin sama - Shugaban Philippines

Shugaban Philippines Rodrigo Duterte
Bayanan hoto,

Shugaba Duterte ya fara gangamin yaki da cin hanci da rashawa a kasar tun bayan hawan sa mulki

Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte, ya ce zai jeho duk wanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa a kasar daga jirgin sama, a cewarsa ya taba yin haka a can baya.

''Idan aka sameka da almundahana, zan sanya ka a cikin helikofta har zuwa birnin Manila, sannan na wullo ka kasa'', inji shi.

Ya yi wannan kalami ne ga mutanen da ibtila'in guguwar da ta afkawa kasar ta shafa, ya kara da yin barazanar daukar mataki ga duk wanda ya yi yunkurin wawashe kayan agajin da ya yi alkawarin kaiwa mutanen yankin.

Wannan shi ne ikirari na baya-bayan nan da shugaban ya yi, kan cewa ya taba harbe mutane a lokacin da yake magajin garin Davao.

A farkon watannan wani mai magana da yawun shugaba Deturte, Martin Andanar ya ce ya kamata mutane su dauki maganar da ya yi da muhimmanci.

Mista Deturte dai ya ce zai dauki matakin ne a wani bangare na kamfe din yaki da cin hanci da rashawa da ya ke jagoranta a kasar.