Muhimman hotunan Afirka na 2016

Zababbun hotuna masu armashi daga nahiyar Afirka na shekarar ta 2016:

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Oscar Pistorius ya cire kafafun sa na roba, kuma ya dungura da dungulmin kafafunsa a cikin kotu a Afirka ta Kudu, a lokacin da ake gudanar da shari'arsa a watan Yuni
Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Sojojin ruwa sun dauki hoton jirgin ruwa da ke dauke da 'yan gudun hijira, a yayin da yake nutsewa a tekun Bahar Rum, tsakanin Libiya da Italiya, inda jami'ai suka ceto 'yan gudun hijira sama da 500
Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A cikin watan Agosta, kananan jirage 20 ne aka ceto daga tekun Libya, inda yawancin su 'yan Eritrea ne da Somaliya, ciki har da wani mutumi dauke da jaririn da aka haifa kwanaki biyar
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zanga a Zimbabwe sun kona tsoffin kudade a Harare babban birnin kasar, domin nuna adawa da shirin da gwamnatin kasar ke yi na fara amfani da takardun kudi, watau 'Bond Notes.
Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A watan Oktoba ne wasu manya da kananan yara mata suka komawa ga iyalansu. Masu fafutukar #BringBackOurGirls ne suka mamaye sunayensu a duniya, bayan sace su da kungiyar Boko Haram ta yi daga makarantarsu da ke Chibok, a Arewa maso gabashin Najeriya a watan Afrilun 2016
Hakkin mallakar hoto Patience Atuhaire
Image caption A wannan kasuwar, gefe daya kasar Uganda ce, daya gefen kuma Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, DRC. Kudin albasa daya ne a duk bangarorin biyu
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lucas Sithole Dan Afirka ta Kudu, ya rungumi Ymanitu Silva dan kasar Brazil, bayan kammala wasan tennis a gasar Olympics ta nakasassu a watan Satumba
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A rana guda kuma 'yan wasan kwallon hannun Rwanda ne suke taken kasa, gabannin karawarsu da China
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A karo na farko kuma tawagar 'yan gudun hijira sun shiga gasar Olympics. Yawancinsu 'yan Sudan ta Kudu suka fito, ciki har da Yiech Pur Biel, da ke hannun hagu
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata alama ta zaman lafiya a Sudan ta Kudu, ita ce wasan dambe na farko da aka yi, tun bayan da yakin basasa ya barke a 2013
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Libya ta yi fama da matsaloli tun rikicin da ya barke bayan 'yan tawayen da ke goyon bayan kungiyar NATO ta hambarar da Kanal Muammar Gaddafi a watan Oktobar 2011. Daga nan kuma mayakan IS suka samu mafaka a kasar, daga bisani kuma dakarun da ke da goyon bayan gwamnati kuma suka shiga yaki da IS din a Sirte a watan Agosta
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zanga da suka bukaci a gyara shirye-shiryen zabe ne suka yi arangama da 'Yan sanda a yankin marasa galihu da ke Kibera a Nairobi babban birnin kasar Kenya, a watan Mayu, inda lamarin ya rutsa da yara 'yan makaranta
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata zanga-zanga ta ba za ta ce ta taso a Zimbabwe cikin shekarar 2016. Bayan da aka tsare wasu masu fafutuka biyu a watan Yuli, masu zanga-zangar dai sun kara da 'Yan sanda a birnin Bulawayo
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu talla a titunan Zimbabwe ma sun yi zanga-zanga, amma 'Yan sanda sun mayar da martani da jefa barkonon tsohuwa, inda mutane suka yi kokarin wanke hayakin daga idanun yara da ruwa
Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Ruwa kamar da bakin kwarya da aka yi a Beledweyne, da ke arewacin Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, ya janyo ambaliyar ruwan da ya tilasta wa daruruwan mutane barin muhallansu
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bayan wasu 'yan watanni, a watan Oktoba, aka dauki hoton wannan babbar motar a kan hanyarta ta zuwa Mogadishu babban birnin kasar Somaliya
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Lahadi ne aka hango wata yarinya ta kahon shanu a garken su da ke Sudan ta Kudu
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A ranar Lahadi ne aka hango wata yarinya ta kahuhunan shanu a garken su da ke Sudan Ta Kudu
Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hauren Giwa kusan 6,700 ne aka kona a filin ajiye dabbobin Nairobi babban birnin Kenya a watan Afrilu
Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Fiye da tan 100 na hauren Giwa ne aka shafe kwanaki ana konawa
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A wani yunkuri na kare Giwayen ne aka yi masu sarka, domin a san inda suke cikin Amboseli National Park da ke Kenya, a watan Nuwamba, sai dai sai an sa su bacci ake iya sanya masu sarkar
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wata cibiyar bincike a Kenya, Mpala, ta dauki hoton wani Gwiwa a yayin da ya ke wasa da laka
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani mai zane dan asalin Tunisia kuma mazaunin Faransa El Seed, shi ya tsara wannan zane a jikin bangon gidanje a unguwar marasa galihu a Cairo babban birnin kasar Masar
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A wani bangaren nahiyar Afirka kuma, wani bikin al'ada ta baje kolin kayan kawa da ake yi duk shekara ta Chale Wote a Accra, Ghana, na cigaba da tasowa
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A watan Nuwamba zaben Amurka ya mamaye nahiyar Afirka, ciki har da 'yan kabilar Massai da ke kusa da garin Saikeri a Kenya, inda suka dukufa suna sauraron sakamakon zaben a rediyo
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A watan Oktoba ne aka bude layin dogon da zai bi ta hanyar Habasha zuwa Djibouti, inda hakan zai yanke tafiyar da a baya ke dauke kwanaki uku, zuwa sa'o'i 12
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yawancin ma'aikatan jirgin 'yan China ne a lokacin da suke tsaka da aiki
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, na bikin murnar cikar sa shekara 92 a watan Fabrairu, inda aka yi masa wani makeken kek
Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A wani gari a Afirka ta Kudu, wanda ake cewa Knysna, an samu wani da ke addinin Rasta, da ya bari mai daukan hoto ya dauke shi yana wani biki na ibada, wanda ya hada da busa hayakin wiwi
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Domin nuna adawa da rashin aikin yi da ake fama da shi a Tunisia, wani mutumi da bashi da aiki ya dinke bakin sa domin yaji da cin abinci a watan Junairu
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Babbar jam'iyyar adawar Ghana watau New Patriotic Party ce ta lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Disamba
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masoya kwallon kafa sun karrama tsohon kociyan Naqjeriya marigayi Stephen Keshi, a Lome, babban birnin kasar Togo a watan Yuni
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Afirka ta Kudu ta yi fama da zanga-zangar dalibai saboda karin kudin makaranta
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wani da ke goyon bayan kungiyar Orange Democratic Movement, ya haska tsakanin wani taro a tsakiyar Nairobi babban birnin kasar Kenya a watan Yuni
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wata gadar jirgin kasa da tabi ta saman rafin Nzi, ya kuma taso ne daga Ivory Coast zuwa Burkina Faso, kuma ya fadi a shekarar 2016, yana nan har yanzu a lalace
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A wani yunkuri na dakile wariyar da Zabiya ke fama da shi, an gudanar da gasar sarauniyar kyau ta zabiya a Nairobi, babban birinin kasar Kenya a watan Oktoba
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu talla a titunan Zimbabwe ma sun yi zanga-zanga, amma 'Yan sanda sun mayar da martani da jefa barkonon tsohuwa, inda mutane suka yi kokarin wanke hayakin daga idanun yara da ruwa

Labarai masu alaka