Nigeria: An cafke shugaban 'yan ta'adda a Legas mai shirin tada zaune tsaye

Yan sandan Nigeria sun cafke wani mutum

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana zargin mutumin da shirin kai hari a wata gada da ke jihar legas

'Yan sanda a Najeriya sun ce sun cafke shugaban wata kungiya, da ke shirya yadda za su tarwatsa babbar gadar sama a birnin Legas.

Jami'an sun kara da cewa sun kuma gano ababen fashewa, da makamai a lokacin da suke gudanar da bincike.

'Yan sanda sun yi ikirarin cewa mutumin da ake zargin, wani jagora ne na masu gwagwarmaya da makamai, kana kwararre ne kan hada abubuwa masu fashewa.

An yi zargin cewa mutumin mai shekaru arba'in da uku, ya shirya tarwatsa babbar gadar nan ce ta Third Mainland Bridge, wadda ta hada yankin harkokin kasuwanci da ke tsibirin, da kuma sauran sassan babban birni mai hada-hada.

'Yan sanda sun ce suna kuma farautar sauran 'yan kungiyar da ke shirin tada zauna tsaye.

Wani jami'i ya ce mutumin da ake zargin yana da alaka da kungiyoyin masu tayar da kayar baya a yankin Niger-Delta mai arzikin mai.

Yankin dai yana fama da hare-hare wadanda suka yi sandiyar raguwar hako man fetur da Nigeria ke yi har kashi daya cikin uku, na adadin man da kasar ke hakowa.