Ba za mu kori jami'an Amurka ko daya ba - Putin

Vladmir Putin da Barack Obama

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dangantaka tsakanin Putin da Obama ta sukurkuce a baya-bayan nan

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya sanar da cewa kasarsa ba zata kori kowa daga cikin jami'an diplomasiyyar Amurka ba a matsayin martani akan abinda ka yiwa jami'an kasarsa su 35 da aka kora.

Mr Putin ya ce zai jira har sai Donald Trump ya karbi mulki a watan gobe sannan zai yanke shawara akan matakin da zasu dauka.

A ranar Alhamis ne gwamnatin shugaba Obama ta bayar da umarnin cewa jami'an diplomasiyar Rasha su 35 su tattara nasu ya nasu a cikin sa'oi 72 su fice daga kasar kuma za a rufe wasu cibiyoyi biyu da suke amfani da su wajen tattara wa kasar bayanan sirri.

Amurka dai na zargin Rasha da yi mata katsalandan a cikin zaben shugaban kasar da aka yi a watan jiya, abinda Rasha ta musanta inda ta ce zargin sam ba shi da tushe.

Tun ba yau ba dai Shugaba Obama wanda Donald Trump zai gada a ranar 20 ga watan Janairun 2017 ya sha alwashin daukar mataki kan Rasha bisa zargin cewa ita ce ta bayar da umarnin yin kutsen.

Amurka ta ce an shiga cikin akwatunan sakonnin e-mail na jam'iyyar Demokrat da kuma ofishin kamfe na Hillary Clinton domin bai wa Mista Trump dama.