Babu shinkafar roba a Nigeria - NAFDAC

Shinkafa
Bayanan hoto,

NAFDAC ta ce gurbatacciyar shinkafa Kwastam ta kwace ba ta roba ba

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta ce sakamakon gwajin da aka yiwa shinkafar da jami'an hukumar kwastam na kasar suka kwace ya nuna cewa shinkafar gurbatacciya ce ba ta roba ba.

Wani babban jami'i a hukumar ya ce shinkafar dai na dauke da kwayar cutar bakteriya ne wadda ta wuce adadin da aka amince da ita.

Jami'an hukumar ta kwastam sun hakikance cewa shinkafar da suka kwace a Lagos a makon jiya ta roba ce, lamarin da ya haifar da cece-kuce har ministan lafiya na kasar ya shiga tsakani yana mai cewa ba bu wata shaida da ta tabbatar da hakan.

Gwajin da aka yiwa shinkafar dai ya tabbatar da cewa amfani da ita zai iya haifar da illa ga al'umma saboda kwayar cutar bakteriyar da ke cikin shinkafar ta wuce kima.

Hukumar kwastam ta ce ta kwace shinkafar ne bisa bayanan da ta samu cewa za a shigo da shinkafar roba mai yawa daga Asiya zuwa Afrika.

Duk da cewa sakamakon gwajin shinkafar ya tabbatar da cewa gurbatacciya ce, har yanzu wasu bayanai sun nuna cewa akwai tan-tan na lalatacciyar shinkafa da aka ajiye a rumbunan tara abinci da ke kasashe makwabta.

Shinkafa dai itace abinci na farko da 'yan Najeriya suka fi amfani da ita, kuma itace akafi bayarwa kyauta idan wani sha'ani ya tasowa mutum.