An bukaci a kawo karshen kisan Musulmi a Myanmar

An kashe mutane akalla 86 a jihar Rakhine da ke Myanmar

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

An kashe mutum akalla 86 a jihar Rakhine da ke Myanmar

Mutum 11 da suka samu kyautar zaman lafiya ta Nobel sun bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta kawo karshen kisan da ake yi wa Musulmi 'yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar.

A cikin wata budaddiyar wasika da suka rubuta, mutanen sun caccaki jagorar gwamnatin kasar Aung San Suu Kyi.

Sun zargi gwamnatin da kokarin kawara da al'umar Musulman na Rohingya, marasa rinjaye.

A cewar majalisar dinkin duniya, fiye da mutum 34,000 'yan kabilar Rohingya aka tursasawa barin gidajensu saboda gujewa ayyukan da sojoji ke yi a jihar Rakhine.

Ana dai zargin Ms Suu Kyi wadda ke da karfin fada aji da gazawa wajen kare kabilu 'yan tsiraru.

Mutanen 11 da suka hada da Archbishop Desmond Tutu da Malala Yousafzai sun rubutawa kwamitin tsaro na MDD wasika cewa "Ana keta zarafin bil-adama matuka gaya a Myanmar.

A dan haka idan har muka gaza daukar matakin da ya dace, to ko shakka babu yunwa za ta kashe mutane idan har ba a harbe su ba".