Bama-bamai sun kashe mutum 28 a Iraqi

An tashi bama-baman ne yayin da kasuwar ke tsaka da ci

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An tashi bama-baman ne yayin da kasuwar ke tsaka da ci

Akalla mutum 28 ne suka mutu sannan wasu mutum 40 suka jikkata bayan wasu tagwayen bama-bamai sun tashi a wata kasuwa da ke tsaka da ci a birnin Bagadaza na kasar Iraqi.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato jami'an 'yan sanda na cewa bama-baman sun tashi ne a kusa da wasu kantunan sayar da kayan motoci a kasuwar al-Sinak.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

Birnin na Bagadaza na ci gaba da fama da hare-haren bama-bamai inda yawancin ake harar wuraren da mutane suka fi taruwa.

Kungiyar IS ta sha daukar alhakin kai irin wadannan hare-hare.

Kungiyar na shan matsin lamba daga wurin dakarun gwamnatin kasar, wadanda suke fatattakar ta daga birnin Mosul inda take da karfi.

Jami'ai sun ce dan kunar-bakin-wake ne ya tashi bam na farko yayin da aka dasa bam na biyu a cikin kasuwar.