Nigeria: Ƙaunar Buhari na neman hada faɗa

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce demokradiyya ta gaji yabo da suka, don haka babu dalilin fada da juna

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce demokradiyya ta gaji yabo da suka, don haka babu dalilin fada da juna

A Najeriya, yayin da aka ga kamun ludayin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, an fara samun saɓanin ra'ayi tsakanin magoya bayansa sakamakon matakin da wasu daga ciki ke ɗauka na sukar wasu manufofin gwamnatinsa.

`Yan ga-ni-kashe-nin shugaban kasar dai na cewa shugaba Buhari ba ya laifi, don haka bai kamata a kushe masa ba, inda sukan maida raddi da kakkausar kalamai idan ana muhawara da su kai-tsaye ko ta shafukan sada-zumunta na zamani, lamarin da ke rage tagomashin shugaban kasar a zukatan masu sassaucin ra`ayi.

Duk da cewa duka ƙaunar mutum guda ce ta haɗa su, masu sassaucin ra`ayi na ganin cewa ba daidai ba ne su yi shiru a duk inda suka ga shugaban kasar ya yi kuskure, saboda a ra`ayin irin waɗannan mutane, mutum tara yake bai cika goma ba, don haka kamar sauran jama'a, shugaban kasar bai fi ƙarfin yin kuskure ba, kuma yi masa gyara ko tsokaci wata siga ce ta ƙauna.

Sai dai ɓangaren shugaban kasar ya ce demokradiyya ta gaji yabo da suka, don haka babu dalilin fada da juna.

Masana dai na ganin cewa magoya bayan shugaba Buhari na bukatar sake-lale a muhawararsu, saboda masu sassaucin ra`ayi na cewa azalzalar da `yan ga-ni-kashe-ni ke musu ta sa ƙaunar da suke yi wa shugaban kasar ta fara gushewa a hankali.