Merkel ta ce Jamus na fuskantar babbar barazana daga 'yan ta'adda

Mrs Merkel ta ce sun fuskanci babban kalubale a shekarar 2016

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Mrs Merkel ta ce sun fuskanci babban kalubale a shekarar 2016

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce kasarta na fuskantar babbar barazana daga wurin 'yan ta'addan da ke ikirarin kishin Musulinci.

Mrs Merkel ta bayyana haka ne a sakonta na sabuwar shekara.

Da take bayani kan harin da wani dan kasar Tunisia ya kai a kasuwar Kirsimeti ta birnin Berlin a wannan watan, Shugabar ta Jamus ta ce abin takaici yadda masu neman mafaka a kasarta suka kai wa mutanen da za su kare su harin ta'addanci.

Ta kara da cewa 2016 shekara ce da suka fuskanci "gwaje-gwaje masu zafi".

Sai dai ta ce ta yi imanin cewa Jamsu za ta magance kalubalen da take fuskanta.

Mrs Merkel ta ce, "A yayin da muke ci gaba da gudanar da rayuwarmu, muna so mu gaya wa 'yan ta'adda cewa: 'Ku mutane ne masu cike da kiyayya masu kashe jama'a, amma ba za ku tsorata mu mu sauya yadda muke gudanar da rayuwarmu ba."

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Motar da aka yi amfani da ita wajen kai hari a Berlin