Buhari ya musanta korar Ibrahim Magu daga aiki

Ibrahim Magu

Asalin hoton, Efcc

Bayanan hoto,

Ibrahim Magu ya sha alwashin yaki da cin hanci ta kowacce fuska

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya musanta rahotannin da wasu kakafen watsa labarai na kasar suka bayar cewa ya kori shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati, EFCC, Ibrahim Magu daga aiki.

Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar ranar Asabar ta ce masu watsa irin wadannan rahotanni suna yin shaci-fadi ne kawai.

A cewarsa, "Mun karanta rahotannin cewa an sallami shugaban EFCC, Ibrahim Magu daga aiki. Babu wani rohoto da babban mai shari'a na kasa, wato Antoni Janar ya mika wa fadar shugaban kasa a kan wannan batu. Don haka rahotannin da ke cewa an kore shi daga aiki shaci-fadi ne kawai".

Ibrahim Magu dai ya shiga bakin 'yan jarida sosai tun bayan da majalisar dattawan kasar taki amincewa ta tabbatar da shi a matsayin shugaban EFCC, tana mai cewa ta dauki matakin ne sakamakon wani rahoton sirri da hukumar tsaro ta farin-kaya, DSS ta mika mata a kansa wanda ke nuna cewa ya aikata ba daidai ba.

Sai dai masu fashin-bakin siyasa na ganin an ki tabbatar da Mr Magu a kan mukaminsa ne saboda takun-sakar da ake yi tsakaninsa da shugaban DSS ba wai domin ya aikata wani laifi ba.

A kwanakin baya ne kakakin shugaban kasar ya ce Shugaba Buhari ya bayar da umarni ga ministan shari'ar kasar ya yi bincike kan wasu manyan jami'an gwamnatinsa bisa zarginsu da aikata ba daidai ba.

Kodayake bai ambaci mutanen da za a yi bincike a kan nasu ba, amma rahotanni na cewa Ibrahim Magu da Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal su ne mutanen da za a yi bincike a kansu.

Shi dai Ibrahim Magu ta taka sawun manyan mutane da dama a yakin da yake yi da cin hanci da rashawa, cikin su har da Kanar Sambo Dasuki, tsohon mai bai wa tsohon shugaban kasar shawara a kan sha'anin tsaro da kuma tsofaffin manyan jami'an rundunar sojan kasar, wadanda ake zargi da sace kudin da aka ware domin yaki da kungiyar Boko Haram.