An kama matuƙin jirgin saman Canada da ya bugu da giya

map of Canada showing Calgary and the capital, Ottawa

An kama wani matukin jirgin saman Canada wanda ya yi tatul da giya yana dab da soma tuka jirgin.

Awowi biyu bayan an kama shi ne, sai aka gano cewa giyar da matukin jirgin mai shekara 37 ya ta ninka sau uku adadin da ya kamata ya sha kafin ya yi tuki.

Daga bisani dai wani matukin jirgin ne ya tuka jirgin da ya kamama mutumin ya tuka inda ya tashi daga filin jirgin saman Calgary ya nufi filin jirgin saman Cancun na kasar Mexico.

Akwai sama da fasinjoji 100 a jirgin.

Lamarin ya faru ne ranar Asabar da karfe 07:00 na safiya a agogon kasar.

Wasu ma'aikatan jirgin ne suka lura da yadda matukin jirgin ke yin nuna wasu halaye da ba a saba gani ba, sai kuma bacci ya dauke shi.

Daga nan ne suka sanar da hukumomi inda aka je aka fitar da shi daga jirgin.

Yanzu dai ana tuhumarsa da laifin kokarin tashi da jirgi alhalin yana cikin maye.

Kakakin rundunar 'yan sanda Paul Stacey ya shaida wa manema labarai cewa za su jira har sai matukin jirgin ya dawo hayyacinsa kafin su gurfanar da shi a gaban kotu.