An harbe ministan muhalli a Burundi

Emmanuel Niyonkuru

Asalin hoton, Government of Burundi

Bayanan hoto,

Emmanuel Niyonkuru na kan hanyarsa ta zuwa gida lokacin da aka harbe shi

Wasu mutane da zargi 'yan bidiga ne sun harbe har lahira ministan muhallin kasar Burundi a lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida a jajiberen sabuwar shekara.

Kakakin rundunar 'yan sandan kasar ya wallafa a shafin Twitter cewa wani dan bindiga ya kashe Emmanuel Niyonkuru, mai shekara 54, da misalin karfe 11:45 na dare a agogon Najeriya da Nijar.

A wani sakon Twitter da shugaban kasar Pierre Nkurikiye ya aike ya ce an kama wata mace da take tare da Mr Niyonkuru a lokacin da aka harbe shi domin a yi mata tambayoyi.

Mr Pierre Nkurunziza ya ce za a hukunta duk wanda aka samu da laifin kisan ministan.

An kashe daruruwan mutane, cikin su har da manyan jami'an soji a rikicin da ya barke a kasar tun lokacin da Shugaba Nkurunziza ya tsaya takara domin yin ta-zarce a karo na uku a shekarar 2015, sabanin yarjejeniyar da 'yan hamayya suka ce an kulla domin ya sauka daga mulki idan ya yi wa'adi biyu.

Amma wannan ne karo na farko da aka kashe wani minista tun da aka soma rikicin.