Koriya ta Arewa za ta gwada makamin ƙare-dangi

Kim Jong-un

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kim Jong-un ya yi wa 'yan kasar jawabin shiga sabuwar shekarar 2017

Shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya ce kasarsa na dab da yin gwajin makaman kare-dangi masu cin dogon-zango wadanda za su iya daukar makamashin nukiliya.

Mr Kim, wanda ya bayyana haka a sakonsa na sabuwar shekara, ya kara da cewa yanzu haka ana gabar karshe ta kammala kera makaman.

Sau biyu Koriya ta Arewa ta yi gwajin makaman nukiliya a shekarar 2016.

Hakan ya janyo fargabar cewa watakila kasar ta sabunta shirinta na kera makaman na nukiliya.

Sai dai ba ta taba yin nasara a gwaje-gwajen da ta yi na makaman ba.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani babban jami'in rundunar sojin Amurka na cewa duk da yake Koriya ta Arewa tana da karfin kera kawunan makaman nukiliya amma ba za ta iya harba su domin cin dogon-zango ba.