Kotun kolin India ta kori shugaban Kurket na kasar

Asalin hoton, Getty Images
Anurag Thakur na da karfin fada aji a harkokin siyasar India
Kotun kolin India ta bukaci shugaban hukumar wasan kurket ta kasar, BCCI, da ya sauka daga mukaminsa sakamakon rashin aiwatar da wasu sauye-sauye.
Anurag Thakur shi ne shugaban babban hukumar Kurket kuma daya daga cikin masu fadi a ji a harkokin wasan a duniya bakin daya.
A shekara ta 2016, kotu ta kafa wani kwamiti da zai bayar da wasu shawarwari domin kawo sauyi a hukumar.
Kotu ta gabatar da kwamitin da zai binciki yadda aka karya dokoki a gasar wasannin Kurket a shekara ta 2013.
An bai wa hukumar ta BCCI nan da kwanaki kadan ta aiwatar da sauye-sauyen da kotun ta nemi a yi.
Sabbin sharudan sun hada da hana ministocin gwamnati tsayawa takarar shugabancin hukumar.
Wasan Kurket shi ne mafi shahara a kasar ta India, kuma ana samun biliyoyin kudi a ciki.