Diego Costa: Saura kiris na bar Chelsea a bana

Dan wasan gaba na Chelsea Diego Costa

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan gaba na Chelsea, Diego Costa, ya ce saura kiris ya bar kulub din a karshen kakar wasannin da ta gabata.

Costa ya koma Chelsea ne kan fan miliyan 32 a 2014, kuma ya yi niyyar komawa tsohuwar kungiyarsa ta Atletico Madrid saboda rashin jin dadin rawar da ya taka leda a kakar 2015-16.

Dan kwallon na Spaniya ya zura kwallo 14 a gasar Premier, inda Chelsea ke saman tebur da tazarar maki shida bayan lashe wasanni 13 a jere.

"Shin ko na so na tafi? Eh, hakika, na so na bar Chelsea. Amma saboda wasu dalilai daban," a cewar dan wasan mai shekara 28.

"Na so na sauya wani abu ga iyalina, amma hakan bai yiwu ba, a don haka a yanzu ina ci gaba da zama cikin farin ciki.

Costa ya zura kwallo 20 a kakar farko da ya yi a Ingila, inda Chelsea ta lashe gasar karkashin jagorancin Jose Mourinho.

Sai dai kwallo hudu kawai ya iya ci har zuwa lokacin da Mourinho ya bar kulob din a watan Disambar 2015.

Dan wasan, wanda haifaffan Brazil ne, ya ce ya yi kokari matuka wurin ganin ya rage halayyarsa ta fushi da fada a lokacin wasa.