Abubuwan da za su faru a Afirka a 2017

An kunna abin tartsatsin wuta na wasa a daren shiga sabuwar shekara a Abidjan

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Bayan kammala bukukuwan sabuwar shekara ta 2017, me zai faru a kasashen Afirka?

A jerin wasikunmu daga 'yan jaridar Afirka, Joseph Warungu, ya yi ishara ga wasu muhimman mutane, wurare da kuma tarukan da ya kamata a saka wa ido a Afirka a 2017.

Afirka za ta fuskanci ayyukan dan adam shida a bana - za ta staya da kafafunta, ta tsuguna, sannan ta tsuguna da guiwowinta, ta rusuna, ta fadi kuma ta tashi tsaye.

Ga yadda za ta yi:

Tsayawa (Trump, Ghana, Habasha)

A jerin wadanda za su kasance a tsaye a Afirka a 2017 shi ne Donald Trump.

E, na san laifin cin amanar kasa ne alakantashi da Afirka.

Amma idan an rantsar da shi a matsayin shugaban kasa, manufofinsa na harkokin waje (ko manufofin Tiwtter) za su yi tasiri kan nahiyarmu. Masu sukarsa sun yi gargadin cewar matsayinshi na kebancewa zai rage kula da Afirka.

Amma kuma zai iya sa 'yan nahiyar su samo mafita daga ciki, ta karfafa ma'aikatanmu, kyautata ababen more rayuwa, aikin gwamnati, tsaro da kuma cinikayya a tsakaninmu.

Wani mutumin da zai hau karagar mulki a watan Janairun kuma shi ne Nana Akufo Addo, zababben shugaban Ghana.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Hotunan Nana Akufo-Addo ne a jikin wasu riguna da wasu mutane suka sanya a lokacin bukukuwan sabuwar shekara ta 2017 a Ghana

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ya fara kokarin shiga fadar shugaban kasa ta hanyar akwatin kuri'a a matsayin dan takaran jam'iyyar New Patriotic Party tun shekarar 2008.

A yanzu da ya samu makullin, 'yan Ghana za su jira su ga yadda zai cika alkawarin gunduma daya, masana'anta daya don kar ya zama mutum daya, wa'adi daya.

Kuma akwai dokar-ta-baci a Habasha wadda ta ke a tsaye. An tsayar da ita ne a watan Oktobar bara bayan wasu jerin zanga-zangar tashin hankali.

Gwamnatin ta ce an samu ci gaba a harkar tsaron in banda wasu-taho-mugama a Arewacin yankin Amhara.

Tsugunawa da guiwowi - Kagame, Kenyatta, Tarayyar Afirka.

Akwai shahararrun mutum biyu wadanda za su tsuguna da guiwowinsu gaban masu zabe domin neman aiki.

Paul Kagame ya kasance shugaban kasa a shekara 16 da suka wuce, amma da alaman 'yan Rwanda basu gaji da shi ba kuma sun zabi dauke wa'adin mulki a kasarsa.

Saboda haka, a watan Agusta, Mr Kagame, zai yi amfani da damarsa ta kundin tsarin mulki domin neman wani sabon kwantiragin aiki.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame a hagu da kuma takwaransa na Kenya Uhuru Kenyatta dukkanninsu suna neman a sake zabarsu a 2017

A cikin watan ne kuma, makwabcinsa na kasar Kenya Uhuru Kenyatta, zai sake neman aikinsa.

Zai bayyana a watan Augusta idan 'yan Kenya za su baiwa Jubilee karin lokacin shagali, ko kuma a'a.

Kungiyar Tarayyar Afirka tana neman sabon shugaban zartarwa kuma za ta cika gurbin a watan Janairu.

Mazaje uku da mata biyu daga Bostwana, Kenya, Chadi, Senegal da kuma Equatorial Gueinea za su kara domin maye gurbin 'yar Afirka ta Kudu mai barin gado, Nkosazana Dlamini-Zuma, a matsayin shugabar kungiyar.

Tsugunawa, Najeriya, Gambia

Yanzu ga wasu yanayi da kuma mutane da ba za su iya yanke shawarar tsayawa ko kuma zama ba.

Tattalin arzikin Najeriya ya kamu da ciwon ciki mafi wahala a cikin shekara 20. Saboda haka ta shigo shekarar 2017 a tsugune.

Dalilai da dama, ciki har da faduwar farashin mai a kasuwar duniya, wadda Najeriya ta dogara akai sosai, da kuma faduwar darajar naira, kudin kasar, sun yi tasiri wajen haddasa mummanan koma-bayan tattalin arzikin kasar a shekara 2016.!"

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Akwai sauran rina a kaba a bangaren tattalin arzikin Najeriya

A kasar Gambia kuma Yahaya Jammeh ba kamili ba ne - ya zabi tsugunawa a gidan gwamnati.

Ya sha kaye a zaben shugaban kasa a hannun Adama Barrow kuma ya amince da shan kayen a bayyane.

Daga baya, tunanin barin kujerar da ya kira shekara 22 da suka wuce ya fi karfinsa, kuma ya sauya shawara.

Afirka da duniya ta ce masa ya koma gida, amma ya hau kujerar naki.

Rusunawa - Laberiya, Angola da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Akwai sanannun mutum uku da za su rusuna daga karagar mulki a shekarar 2017.

Elllen Johnson-Sirlef, mace ta farko da aka fara zaba a matsayin shugabar kasa a Afirka, tana kusa da karshen wa'adinta na biyu kuma na karshe a Laberiya.

Daya daga cikin wadanda suke jira a bayan fili domin shiga takarar maye gurbinta shi ne tauraron kwallon kafar nan, George Weah.

Tsohon dan wasan gaban AC Millan da Chelsea ya kasa lashe zaben a shekarar 2005, amma yana fatan shekarar 2017 za ta kasance tasa.

'Yan Angola za su samu damar maye gurbin mutum daya tilon da suka sani a matsayin shugaban kasar kimanin shekara 40.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Yawancin matasa a Congo na fatan Shugaba Kabila zai bar mulki ba tare da fitina ba

Duk da cewar Jose Eduardo dos Santos ya ba da sanarwar cewa zai sauka, jininsa zai cigaba da gudana ta jijiyoyin mulki da tattalin arziki a Angola.

A Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, shekarar 2017 za ta iya kasancewa farkon karshen mulkin wata zuri'a, wadda ta fara mulki a 1997 a lokacin da Laurent Kabila ya zama shugaba bayan yi wa Mobutu Sese Seko juyin mulki.

Dan Laurent Kabila, Joseph, ya hau karagar mulki bayan an kashe babansa a shekara 2001, kuma ya nemi dawwama kan mulki har sai da yunkurin sauya kundin tsarin mulki domin ya samu wa'adi na uku ya ci tura.

Zanga-zanga da tashin hankali sun kara matsin lamba kan Shugaba Kabila da ya bar mulkin a bara kuma batun zai cigaba a sabuwar shekara.

Faduwa - Kudaden makaranta, shugabannin kasa da siket

Haryanzu maudu'in faduwa na raye a Afirka ta Kudu

Gangamin #FeesMustFall wanda daliban jami'a suka yi na yakar hauhawar kudin makarantar gaba da sakandare ya haddasa fada tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga.

Da alaman za a sake samun irin wadannan domin kudaden makarantan basu fadi ba.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A shekarar 2017 za a fi amfani da dogayen kaya maimakon gajeru

Har wa yau wasu jami'o'i sun sanar da karin kashi 8 cikin dari na kudin makaranta.

Kuma akwai batun shugaban kasar, Jacob Zuma.

A watan Disamban 2017, wa'adinshi a matsayin shugaban jam'iyyar ANC mai mulki zai kare, amma wa'adinshi a matsayin shugaban kasar zai kare ne a shekara 2019.

Shin ANC za ta kyale Zuma ya fadi kamar yadda ta kyale shugaba Thabo Mbeki a irin wannan yanayin?

Sehekar 2017 za ta ba da amsar.

A kwai yiyuwar kuma za a fi amfani da dogayen kaya maimakon gajeru a shekarar 2017.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Uganda na fatan zama kasar gabashin Afirka ta farko da za ta ci kofin kasashen Afirka a shekara 55

Tashi- Uganda, Afirka

Gasar cin kofin Afirka za ta soma a tsakiyar watan Janairu a Gabon kuma Uganda na rike da fatan Afirka ta gabas.

Nahiyar na da mummunan tarihi a wasan kwallon kafar Afirka.

A lokacin da Afirka ta yi tuntube, dole ta sake tashi domin yadda ake fada a Najeriya rana tana haska wadanda suke tsaye, kafin ta haska wadanda suke zaune.