Shin ko kai 'Bahaushen' asali ne?

Akan yi wa gine-gine zayyana a garuruwan Hausawa

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Soro a kasar Hausa

A kan yawaita samun mahawara kan ko wane ne 'Bahaushe', tsakanin mutumin da bai san wani yare ba idan ban da Hausa, duk kuwa da cewa asali Hausar ba yarensa ba ce, da kuma wanda shi ba shi da wani yare sai Hausar.

An dade dai ana tafka mahawara kan wannan batu musamman a tsakanin manazarta harshe.

Hakan kuwa ba ya rasa nasaba da irin karfin da yaren na Hausa yake da shi a yankin Yammacin Afirka da ma sauran sassan duniya.

Misali, kasar Ghana, na daya daga cikin wuraren da Hausawa suka yi wa tsinke shekaru aru-aru sakamakon cirani da kuma lokacin yakin duniya.

Wannan ne ya sanya Hausa ta zama yaren da kusan mafi yawancin al'ummar arewacin Ghana kan yi ko da kuwa suna da yarensu na asali.

Har ta kai ga ma'aurata, a yankin kan auri juna ba tare da daya na jin yaren daya ba, a inda Hausa kan zama ita ce yaran da suke magana da juna.

A wani lokaci ma a kan samu yanayin da 'ya'ya ba sa iya yaren mahaifan nasu sai Hausa saboda iyayen ba sa fahimtar yaren juna.

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Mabusan algaita a kasar Hausa

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai, a wata ziyarar aiki da ya kai birnin Kumasi na Ghana, ya zanta da irin wadannan ma'aurata dangane da yadda Hausar ta yi tasiri a kansu da kuma yadda ake zaman lafiya da juna a kasar duk da banbanci addini da kabila.

Ma'auratan wadanda ba sa jin yaren juna sun ce "kadan-kadan muke jin yaren juna", a inda kuma kowanne daga cikinsu ya yi sauri ya ce "amma idan yara suka zo to yarena za su yi."

Miji da matar dai sun ce suna yin yaren Hausa ko kuma na Ashanti a tsakaninsu.

Kusan za a iya cewa irin wannan yanayi na birnin Kumasin Ghana yana faruwa a wasu sassa daban-daban na Najeriya da Niger da Kamaru da Chadi da Sudan da dai sauransu.

Kididdiga dai ta nuna cewa masu magana da yaren Hausa a duniya wadanda ba asalin Hausawa ba ne sun yi kan-kan-kan da Hausawan da suka gaji yaren.

Wasu ma na ganin yaren Hausa ya zama irin na Turanci wanda kowane mutum kan iya lakantar sa har ma ya fi dan asalin yaren iyawa da ma cin moriyarsa.

Ana dai ganin karbuwar Hausa a duniya ba ta rasa nasaba da irin zaman lafiya da masu yaren ke yi da bakinsu ko kuma wadanda suka sauke su.