Trump: Korea ba za ta iya kera makamin da zai kai Amurka ba

Makamin nukiliyar Koriya ta Arewa
Bayanan hoto,

Ba wannan ne karon farko da Koriya ta Arewa ke ikirarin kera makami mai cin dogon zango ba

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya musanta ikirarin da Koriya ta Arewa ta yi cewa za ta iya kera makamin nukiliya mai cin dogon zango da zai iya kaiwa Amurka.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Trump ya ce maganar da Shugaba Kim Jong Un ya yi a lokacin shirye-shiryen bikin sabuwar shekara na kaddamar da nukiliya ba shi da tushe bare makama.

Ya kara da cewa "Sam hakan ba zai yiwu ba".

Abin da ba a tantance ba shi ne ko yana shakka game da kalaman Shugaban Koriya ta Kudun ko kuma yana shirin daukar matakin kare Amurka ne.

Trump ya kara da sukar China saboda gazawarta wurin matsa lamba a kan aminiyarta ta takaita shirinta na nukiliya.

Ya kuma zargi hukumpmomin kasar ta China da samun makudan kudade a huldar kasuwancinta da Amurka, wacce ya ce bangare daya ne (China) kawai ke amfana.

Koriya ta Arewa ta dade tana ikirarin mallakar makami mai dogon zango, sai dai babu tabbas a kan gaskiyar ikirarin nata.