Habasha ta yanke wa Musulmai hukunci kan ta'addanci

Kotu a Habasha
Bayanan hoto,

An yanke hukuncin ne dan yaki da tsattsauran ra'ayi da gwamnati ke yi

Kotun gwamnatin tarayyar Habasha ta yanke wa mutane 19 daga cikin 20 hukuncin daurin shekara biyar da wata shida a gidan kaso, ya yin da ta yanke wa dayan hukuncin daurin shekara hudu saboda la'akkari da rashin lafiyar da ya ke fama da ita.

Tun a shekarar 2014 aka gurfanar da mutanen gaban kuliya, amma sai a watan jiya ne kotun ta same da aikata laifin da ake zargin su da shi.

An kama su ne shekara uku da suka wuce kan zanga-zangar kin tsoma hannun gwamnati cikin harkar addini.

Ko a watan Agustan shekara 2015 ma wata kotu ta yanke wa Musulmi 18, ciki harda malamai da wani dan jarida, hukuncin daurin shekara 22 karkashin dokar hana ta'addancin nan mai yawan janyo cece-kuce a kasar.

An dade ana zargin gwamnatin Habasha da hana 'yan adawa fadin alabarkacin bakinsu, amma gwamantin na musantawa.