Dan Ghana ya baje kolin kayan da ya kera

Fiye da shekaru 16 kenan da kamfanin Kantanka ya kera mota ta
Wani dan kasar Ghana ya baje kolin sabbin kayan da ya kirkira da suka hada da motoci a bikin baje kolin kimiyya da fasaha da aka yi a garin Gomoa Mpota da ke birnin Accra.
Kwadwo Sarfo dai shi ne ya kirkiri cibiyar kimiyya da fasaha ta Kantanka Technplogy Centre for Excellence, wadda suka kera babur mai kafa uku, da injin yin walda, da na'urar da ke sansanar hayaki da sauransu, a cewar kafar labarai ta Joys News.
Shugaba mai jiran gado Nana Akufo-Addo wanda ya halarci bikin ya ce gwamnatinsa za ta maida hankali akan wayar da kan 'yan Ghana kan muhimmancin kimiyya da fasaha.
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Internet, Mista Sarfo ya fara gwada fasaharsa ne da yin gangunan da suke amfani da wutar lantarki, da lasifika, da yin akwatin talabijin mara tudu da sauransu.
Sannan a shekarar 1998 ya kera motar shi ta farko, kuma tun daga wannan lokaci ne kamfanin ya ci gaba da kere-keren kayan zamani.
A bara ne kuma dan shi, wanda ke kula da kamfanin ya shaida wa mujallar New Africa Magazine cewa kamfanin su ya samu lasisin fara kera kayan da za a dinga fitarwa dan sayar wa a kasashen waje.
A bangare guda kuma ana nuna damuwa kan rashin tallafawa kamfanin Kantanka da gwamnatin kasar Ghana ba ta yi.

Asalin hoton, Myjoyonline.com
Kamfanin Kantanka ya samu lasisin fara fitar da fasahar shi kasashen waje

Asalin hoton, Myjoyonline.com
Daya daga cikin motocin da kamfanin Kantanka ya kera

Asalin hoton, Myjoyonline.com
Kantanka ya fara kera motarsa ta farko fiye da shekara 16 da ta gabata