Shugaban hukumar zaben Gambia ya 'tsere'

Asalin hoton, Reuters
Mista Njai ya musanta ikirarin Shugaba Jammeh na cewa an yi magudi a zaben
Iyalan shugaban hukumar zaben kasar Gambia, sun shaida wa BBC cewa ya buya ba a san inda ya shiga ba.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa Alieu Momar Njai ya arce daga kasar, saboda an fara yi masa barazana tun bayan da ya sanar da shan kayen Shugabar Yahya Jammeh a zaben da ya gabata.
Da farko dai Mista Jammeh ya amince da shan kaye inda ya taya Adama Barrow, wanda ya yi nasara murna.
Amma daga bisani ya tubure ya ce bai amince da sahihancin sakamakon zaben ba.
Jami'an tsaro sun mamaye hedikwatar hukumar zaben jim kadan bayan da Mista Jammeh ya sanar da shawararsa ta kin amincewa da sakamakon.
Tarayyar Afirka da Ecowas da Majalisar Dinkin Duniya sun ce lallai ne Mista Jammeh ya mutunta kundin tsarin mulkin kasar ta Gambia.
A ranar 19 ga watan Janairu ne wa'adin Mista Jammeh, wanda ya hsafe shekara 22 yana mulki, zai zo karshe.