Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ya bukaci Trump ya daina wauta

Mr Trump ba ya sanya wa bakinsa linzami

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Mr Trump ba ya sanya wa bakinsa linzami

Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ya bukaci shugaban kasar mai jiran gado Donald Trump ya san cewa "ya girma" sannan ya caccake shi saboda sukar da ya yi wa jami'an tsaron kasar.

A ranar Juma'a ne za a yi wa Mr Trump bayani kan zargin kutsen da ake yi wa Rasha a harkokin zaben da ya wuce na Amurka - koda yake Trump ya sha musanta cewaa Rasha ta yi tasiri a zaben da aka yi masa.

Mr Biden ya ce ba karamar wauta ba ce a ce shugaba mai jiran gado bai amince da abubuwan da jami'an tsaro suka fada ba.

Ita ma Rasha ta musanta yin kutse a sakonnin imel na jam'iyyar Democratic gabanin zaben da aka yi a watan Nuwamba.

Ranar Alhamis ne Mr Trump ya karyata bayanan da jami'an tsaron suka fitar inda suka nuna yadda Rasha ta yi kutse a harkokin zaben kasar.

Abin da Mr Biden ya ce

A wata hira da ya yi da kafar watsa labarai ta PBS, Mr Biden ya ce, "Babban abin kunya ne ga shugaban kasa mai jiran gado kin amincewa da bayanan sirrin da hukumomin leken asiri irin su CIA suka gabatar masa.

"Idan yana tunanin cewa ya fi hukumomin leken asirin sanin aikinsu, kamar yana cewa ne 'na san ilimin kimiyya fiye da malamanina'.

Da aka nemi ra'ayinsa kan yadda Mr Trump ke yawaita yin amfani da Twitter wajen sukar mutane, Mr Biden ya ce: Ya kamata "Donald ya san cewa ya girma, yanzu ba lokaci ba ne da zai rika yin wauta da yarinya saboda shi shugaban kasa ne. Lokaci ne da zai nuna cewa zai yi aikin da aka zabe shi ya yi."

Sai dai ya ce Mr Trump "mutumin kirki ne".