Apple ya janye manhajar jaridar New York Times daga China

New York Times

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jaridar New York Times tana cikin fitattun kafafan yada labaran kasashen yamma da aka sani a duniya

Kamfanin Apple ya janye jaridar New York Times daga jerin manhajojin da yake samarwa a China bayan mahukuntan kasar sun gabatar da bukatar hakan.

Jaridar ta bayyana wannan a matsayin wani yunkurin hana masu karatu a China samun abin da ta kira labaran gaskiya da babu son zuciya.

Kamfanin Apple ya ce an sanar da shi cewa manhajar ta karya dokokin China, amma bai bayyana dokokin da ta karya ba.

Kafafen watsa labaran kasashen yamma sun dade suna fuskantar matsaloli wajen samar da labaransu a China inda ake yawan dakile su.

New York Times ta ce Apple ya cire manhajojinta na Ingilishi da harshen China daga shagonta na intanet a ranar 23 ga watan Disamba.