Wani jariri ya mutu a Faransa bayan an ba shi Bitamin D

Uvesterol D Bitamin D

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ana sayar da maganin Uvesterol D mai dauke da bitamin D a Faransa tun 1990

Jinjiri mai kwana goma a duniya ya mutu bayan an ba shi maganin Uvesterol D, wanda ake amfani da shi a Faransa domin kare yara 'yan kasa da shekara biyar daga karancin sinadarin bitamin D.

Hukumar kula da lafiya a kasar ta ce mai yiwuwa amfani da wannan sinadarin ne ya sa hakan.

A ra'ayin wasu ma'aikatan hukumar akwai wasu sinadarai daban da za a iya amfani da su.

Ministar kula lafiya, Marisol Touraine, ta ce sinadarin bitamin D ba shi da hatsari ga yara, sai dai yadda ake amfani da shi ka iya kawo illa.

Ta kuma yi alkawarin bai wa iyayen yara bayanai na gaskiya a kan lamarin.

Marisol Touraine

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ministar kula da lafiya Marisol Touraine ta tabbatar wa iyayen yara cewa babu wani hatsari ga amfani da sanadarin bitamin D

Wata sanarwa daga Hukumar kula da lafiya a Faransa ta ce an samu matsalar amfani da abin da ake diga maganin da shi.

Hukumar ta kara da cewa a shekara ta 2006 ta dauki matakai na rage hadarin amfani da sinadarin Uvesterol D bayan an ga lahanin maganin. Sai dai har watan Disamba ba wanda ya mutu sakamakon amfani da maganin tun da aka fara sayar da shi a 1990.

Jinjirin ya mutu ranar 22 ga watan Disambar shekara da ta wuce bayan da aka ba shi sinadarin da abin diga magani. Ya nuna alamar shakewa kafin ya mutu sa'a biyu bayan ya kamu da bugun zuciya.