Ana ci gaba da Ja-in-ja tsakanin Obama da Trump kan Obamacare

Barack Obama da Donald Trump a ganawarsu ta farko

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Obama ya yi imanin 'yan majalisar na iya yin wannan yakin da duk iya karfinsu, kuma su yi nasara''

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi kira ga 'yan majalisar dokokin kasar daga jam'iyyarsa ta Demokrat da su tashi haikan su kare tsarin inshorar kiwon lafiyar da gwamnatinsa ta fito da shi; wanda gwamnatin Trump ta sha alwashin soke wa.

A cikin wata ganawa ta sa'oi biyu da 'yan majalisar ranar Laraba, Mr. Obama ya nemi goyon bayan 'yan jam'iyyar tasa kan su hana 'yan Refublika kawar da wannan tsarin nasa.

Ganawar ta biyo bayan da mataimakin shugaban kasar mai jiran gado, Mike Pence, ya je majalisar inda ya shaida wa 'yan jam'iyyarsu ta Refublika cewa gwamnatinsu za ta sauya wannan tsarin.

Bayan ziyarar da shugaban barin gado ya kai harabar majalisar, dan majalisar wakilai na jam'iyyar Demokrat Elijah Cummings ya shaida wa manema labarai cewa Mr. Obama ya nemi da su tashi haikan su kare wannan manufar tasa.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

'Yan majalisar na Demokrat sun yi barkwanci da taken Donald Trump na ''Make Amerika Great Again''

Wadannan kalaman nasa sun zo ne bayan da 'yan jam'iyyar ta Refublika da ke majalisar dattawa suka dauki matakin farkon na soke tsarin kiwon lafiyar da aka fi sani da Obamacare.

Sun jefa kuri'a amincewa da wani kuduri a kasafin kudi da aka tsara da manufar zaftare kudade ake warewa tsarin.

Wannan tsarin kiwon lafiyar dai ya fadada hanyoyin samun inshorar kiwon lafiya ga Amurkawa Miliyan 20 wadanda ba su iya samunsa in ba don tsarin ba.

Amma tsarin - wanda aka fito da shi tun a shekara ta 2010 - ya gamu da cikas na karuwar tsadar kudaden da ake biya da kuma janyewar manyan kamfanonin da ke bayar inshorar ta lafiya, abin da ya bar Amurkawan da zabi maras yawa kan kiwon lafiya.