Cutar mantuwa ta fi kama masu zama daf da titi — Bincike

Traffic

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Binciken bai ce kai tsaye zama kusa da tituna ce ke haddasa cutar mantuwa ba

Wani bincike da aka wallafa a mujallar Lancet ta Burtaniya ya ce mutanen da ke zama daf da titi sun fi shiga hatsarin kamuwa da cutar kidimewa.

Kimanin kashi 11 cikin 100 na masu fama da cutar mantuwa da ke zaune cikin mita 50 daga babban titi na da alaka da hada-hadar abubuwan hawa, a cewar binciken.

Masu binciken - wadanda suka bibiyi rayuwar mutum miliyan biyu a Kanada tsawon shekara 11 - sun ce gurbatacciyar iska da hayaniyar ababen hawa ka iya sa dakushewar kwakwalwa.

Kwararru a kan cutar mantuwa a Burtaniya sun ce akwai bukatar kafa hujja don tabbatar da bincike, ko da yake yana da "kanshin gaskiya".

'Karuwar Jama'a'

Kimanin mutum miliyan 50 ne ke fama da cutar mantuwa a duniya, kuma ba a iya gano abubuwan da ke raba mutane da tunani da kaifin kwakwalensu ba.

Binciken ya gano mutum 243,611 da ke fama da cutar cikin mutum miliyan biyu, amma wadanda suka fi hatsarin kamuwa da ita na rayuwa ne daf da manyan tituna.

Masu binciken sun kuma yi la'akari da karin wasu sabubba irin su fatara da taiba da matsayin ilmi da shan taba wajen janyo cutar mantuwa.

Shawara mafi alheri don rage kasadar kamuwa da cutar mantuwa shi ne yin abubuwan da muka san suna inganta lafiyar jiki - daina shan tabar sigari, motsa jiki da cin lafiyayyen abinci.