An gano riga-kafin karya lagon sauro

malaria

Asalin hoton, SPL

Bayanan hoto,

Kwararru sun ce hanyar ba mai yiwuwa ba ce a zahiri, don kuwa ana bukatar cizon sauro kimanin 200 daga sauro mai yada cutar.

Wani riga-kafin zazzabin cizon sauro ya samu gagarumar nasara a gwajin da aka yi wa Dan adam.

Likitoci sun yi amfani da wani nau'in sauro da aka jirkita kwayar halittarsa ta yadda ba ya harbin mutane da cutar.

Gwaje-gwajen wadanda aka wallafa a mujallar Science Translational Medicine sun nuna cewa riga-kafin na da aminci kuma yana bai wa jiki kyakkyawar garkuwa.

Kwararru kan sha'anin cutukan da ake samu a kasashe masu zafi sun bayyana binciken a matsayin "abin amfani".

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dubban mutane na mutuwa sakamakon cizon sauro a duniya.

Jami'ai a cibiyar bincike kan cutuka masu yaduwa a Seattle sun cire wasu kwayayen halittu guda uku a jikin sauro ta yadda ba zai iya harbin kwayoyin halittar hanta da cuta ba.

Mutum goma aka yi wa gwajin don tabbatar da amincin riga-kafin, a cikinsu ba wanda ya kamu da zazzabi kuma maganin ba shi da wata matsananciyar illa.

Wani kwararre, Sir Brian Greenwood na cibiyar tsafta da magungunan kasashe masu zafi ta London ya ce abin yana da karfafa gwiwa, amma shi matakin farko ne na samun wata allurar riga-kafi.