Ana shirin jibge bataliyar soji 2 a kudancin Kaduna

Sojojin Nigeria na sintiri bayan wani rikici a Kaduna

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Yanzu haka dai akwai sojojin da ke shawagi a sama a sassan da fitinar ke saurin tashi

Rundunar Sojin Nigeria na shirin girke karin bataliyar soji biyu a kudancin jihar Kaduna domin dakile wutar rikicin kabilanci da addini da ta ki ci ta ki cinyewa a can.

Wannan na daga cikin matakan da Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a dauka da manufar kawo karshen salwantar da rayukka da dukiyoyin jama'a da ake ci gaba da yi a can - kamar yadda wata sanarwa daga fadarsa ta bayyana.

Sanarwar ta ce wannan kari ne bisa ga kafa wata rundunar 'yansandan kwantar da tarzoma da aka yi a yankunan da ake saurin samun rikicin.

Haka ma shugaban kasar ya umarci hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar wato Nema; da ta yi nazari kan halin da ake ciki domin sanin irin daukin da za a kai wa wadanda rikicin ya rutsa da su.

Rayukka da dukiyoyi masu dimbin yawa ne ke salwanta a yankin sakamakon hare-hare masu alaka da kabilanci da addini da ke faruwa lokaci zuwa lokaci.