An daure 'yan damfarar da suka kafa bankin bogi a China

Asalin hoton, NANJIN BROACAST STATION
Mutanen 2 , Zeng da He, sun damfari abokan huldarsu dala miliyan 60.
An daure wasu mutane biyu a lardin Nanjing na kudancin kasar Sin bayan samunsu da laifin kafa banki na bogi inda suka damfari mutane miliyoyin daloli.
Kafafen watsa labaran kasar sun ce mutanen sun yaudari abokan huldarsu ne da alkawurran samun riba ninkin-ba-ninkin idan suka ajiye kudi a bankin.
Rahotanni sun ce sun tsara ginin bankin na bogi ne ya yi kamar daya daga cikin bankuna mallakar gwamnatin kasar ta Sin.
''Ma'aikatansu da ke saka kaya na bai-daya wato Uniform da kuma takardun rubuta kudin da mutum zai a jiye, duk sun yi kama da na wasu bankunan kwarai da ake da su a kasar; kodayake bankin nasu na bogi ne,'' In ji wakilin BBC a birnin Beijing.
A yanzu dai mutanen na can a daure - daya na tsawon shekaru tara dayan kuma na tsawon shekaru tara da rabi.
Kafafen watsa labaran gwamnati sun ce mutanen biyu, Zeng da He, sun damfari abokan huldar na su dala miliyan sittin.