Sojoji sun bude wuta a wasu biranen Ivory Coast

Close up of a soldier from Ivory Coast's Republican Forces as he stands guard near the paramilitary police barracks in the Yopougon district in the west of the city of Abidjan on December 21, 2012.

Asalin hoton, AFP

An ji karar harbe-harebn bindigogi a birane biyu na kasar Ivory Coast sakamakon wani abu da ake gani bore ne da wasu sojojin kasar suka yi.

Sojoji da mazauna biranen sun tabbatar da jin harbe-harben.

Sojojin da ke boren sun kwace makaman da aka ajiye a wasu ofisoshin 'yan sanda a Bouake, birni na biyu mafi girma sannan suka ja daga a kofar shiga birnin.

Kazalika rahotanni sun ce an ji karar harbe-harben bindigogi a garin Daloa da ke yammacin kasar.

Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya karbi mulkin kasar ne a shekarar 2011 bayan an gama yakin basasa.

Birnin Bouakena cikin cibiyoyin da aka yi amfani da su wajen kawar da tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo, wanda yanzu haka ake yi wa shari'a a kotun aikata manyan laifuka ta dunia, daga mulki.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wani malamin makaranta a Bouake, Ami Soro, yana cewa yanzu haka mutane sun tsere daga birnin.

Har yanzu ba a san dalilin da ya sa sojojin ke yin bore ba, amma kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce da alama suna yin boren ne saboda ba a biya su albashi ba.

AFP ya ambato wani soja da ba ya so a ambaci sunan sa yana cewa, "Tsofaffin mayakan sa-kan da aka dauke su aikin soja ne ke yin bore domin su bukaci a ba su alawus na $8,000."