Putin 'ya bukaci' ya taimaka wa Trump cin zaben Amurka

Hukumomin leken asiri sun yi wa Donald Trump jawabi ranar Juma'a

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Hukumomin leken asiri sun yi wa Donald Trump jawabi ranar Juma'a

Wani rahoto da hukumomin leken asirin Amurka suka fitar ya nuna cewa shugaban Rasha Vladimir Putin ya nemi ya taimaka wa Donald Trump domin ya lashe zaben da aka yi a watan Nuwamba.

Rahoton ya ce shugaban na Rasha ya "bayar da umarni" ga jami'ansa domin su taka rawar da za ta kai ga cin nasarar Mr Trump.

Hukumomin kasar Rasha ba su ce komai game da wannan zargi ba, sai dai a baya Rasha ta sha musanta zargin.

Bayan hukumomin leken asirin Amurkan sun yi wa Mr Trump bayani kan sakamakon binciken da suka gudanar, shugaban mai jiran gado ya ce rawar da Rasha ta taka a zaben ba ta yi tasiri a kan sakamakonsa ba.

Daga baya kuma Mr Trump ya dora alhakin kutsen da Rasha ta yi a kan "rashin mayar da hankali a aiki" daga bangaren kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar Democrat.

Yanzu dai kwamitin kula da harkokin gida da tsaro na Amurka ya bayar da sanarwar cewa za a tsaurara tsaro kan na'urorin zabe domin kaucewa sake aukuwar hakan.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Donald Trump ya ce zai yi kawance da Rasha da shugaban ta Vladimir Putin