Amurka ta shaida Rashawan da suka yi mata kutse

US

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kafafen yada labaran Amurka sun yi zargin cewa lamarin har da fadar White House ya shafa

Amurka ta ce ta gane jami'an Rasha da take jin su ne suka yi mata kutsen intanet, kafin zaben shugaban kasar wanda Donald Trump ya lashe a watan Nuwambar bara.

An zargi jami'an wadanda ba a fitar da sunayensu ba, da aika sakonnin imel da aka sato na jam'iyyar Dimokrat ga Wikileaks a kokarin murde kuri'u don Mista Trump.

Rasha dai ta musanta duk wani hannu yayin da shi kuma mai Wikileaks, Julian Assange, ya ce ba Rasha ce ta ba shi bayanan ba.

Jami'an leken asirin Amurka na sa ran yin bayani ga Shugaba Trump wanda ke tantama a kan ikirarin kutsen.

Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden ya kyari Mista Trump a kan sukar ma'aikatan leken asirin kasar kan wannan ikirari, ya ce "kwata-kwata babu hankali" rashin amanna ga hukumomin.

Joe Biden ya ce ya karanta rahoton sirrin wanda ya fayyace hannun Rasha, kuma an ga karin bayanan rahoton na fita a kafofin yada labaran Amurka.

CNN da jaridar Washington Post sun fada ta hanyar kafa hujja da majiyoyin leken asiri, cewa hukumomi sun tarbe wasu bayanai, bayan zaben Amurka da ke nuna manyan jami'an Rasha na murna kan nasarar da Donald Trump ya samu.