Nigeria: Tsohuwar ministar mai ta mika dala miliyan 153 ga EFCC

Deizani Alison-Madueke

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ko a shekara ta 2015 hukumar binciken manyan laifuka ta Burtaniya NCA ta binciki Misis Madueke.

Tsohuwar Ministar albarkatun mai ta Nigeria Diezani Alison-Madueke ta mika wa gwamnatin kasar dalar Amurka miliyan 153 da ake zargin ta sata daga asusun gwamnati.

Hakan dai ya biyo bayan wani hukunci da wata kotu ta yanke a birnin Legas ranar Jumu'a cewa matar ta mika wadannan kudaden ga gwamnatin har a tabbatar da halaccinsu ko akasin haka.

A cewar hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa ta EFCC - wadda ita ce ta bukaci kotun da ta umarci tsohuwar ministar ta mika kudin - an sace kudin ne daga kamfanin mai na NNPC kana aka boye su a wasu bankuna uku da ke kasar.

Kamfanin dillancin labaran kasar NAN ya ce Alkalin kotun Muslim Hassan wanda ya ba da wannan umarnin; ya bai wa jami'an bankunan uku wa'adin kwanakki 14 su bayyana gabansa domin su kawo masa shaidar da ke nuna cewa kudin ba na sata ba ne.

Ya ce idan suka kasa yin hakan to za a sallama kudin kacokan ga gwamnatin tarayyar Najeriya.

'Yadda aka saci kudin'

A cikin bukatar neman mika kudaden wadda jami'in bincike na hukumar ta EFCC Moses Awolusi ya gabatar wa kotun, hukumar ta ce a watan Disamba na shekara ta 2014 ne tsohuwar ministar ta kira babban manajan daya daga cikin bankunan a ofishinta suka tsara yadda za a saci kudaden.

Jami'in hukumar ya yi zargin cewa Mrs Diezani Alison-Madueke ta bukaci babban manajan bankin da ya tabbatar da cewa ba a saka kudin a cikin asusun da aka san da zamansa ba kuma ba a rubuta shigar da kudin ba cikin kundin da bankin ke rubuta huldodin da ya yi ba.

Rahoton na kamfanin dillancin labaran Najeriyar dai bai fadi ko lauyoyin tsohuwar ministar suna a kotun lokacin wannan zaman ba; balle martanin da suka mayar ga wadannan zarge-zargen.

Amma dai wannan ba shi ne karon farko da ake zargin ministar da almundahana ko facaka da kudaden jama'a ba, amma kuma a kodayaushe takan musanta.