An kashe mutum 15 a kan iyakar Syria da Turkiyya

Map

Rahotanni sun ce akalla mutum 15 suka mutu sakamakon wani harin bam da aka kai a garin Azaz da ke hannun 'yan tawaye da ke kan iyakar Syria da Turkiyya.

A kwanakin baya 'yan kungiyar IS da ke ikirarin kishin Musulinci sun kai wa garin hari.

An kai harin ne a daidai lokacin da aka tsagaita wuta a rikicin kasar ta Syria bayan Rasha da Turkiyya sun sanya baki.

Ana ci gaba da aiki da yarjejeniyar tsagaita wutar, koda yake ana saba mata a wasu lokutan.

Haryanzu ba a san kungiyar da ta kai harin na na ranar Asabar ba, wanda, wasu rahotanni ke cewa ya yi sanadin kashe fiye da mutum 60 da jikkata mutane da dama.

ISta yi yunkuri sosai na kwace garin, wanda ke hannunta a shekarar 2013.