TFL na kokarin karshe na kauce wa yajin aikin ma'aikatan jiragen kasa a London

Tambari tashar jirgin kasa na karkashin kasa

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Ana jin yajin aikin ya fi shafuwar tsakkiyar birnin

Kamfanin zirga-zargar jiragen kasa mafi girma a Ingila TFL ya yi wa kungiyoyin ma'aikatansa wani sabon tayi, a kokarin da yake na hana su shiga yajin aiki ranar Lahadi.

Babu dai karin bayani game da yunkurin na karshe domin kauce wa yajin aiki wanda kungiyoyin suka shirya domin nuna rashin amincewa da shirin kamfanin na rufe ofisoshin sayen tikiti.

Tayin dai na zuwa ne bayan kungiyar ma'aikatan jiragen kasa mafi girma RMT ta fice daga inda ake wata tattaunawar sulhu ranar Assabar.

Ana sa ran yajin aikin na tsawon sa'o'i 24 - wanda aka tsara zai soma daga karfe shida na yamma ranar Lahadi - ya haddasa rurrufe tashohin jiragen.