Ivory Coast: Boren soji ya bazu zuwa Abidjan

Wasu sojoji kenan a tsaye bayan ministan tsaro (a tsakiya)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Masu boren dai sun yi watsi tayin gwamnati na sasantawa

Wani boren soji da ake yi a kasar Ivory Coast ya bazu zuwa babban birnin kasuwancin kasar Abidjan.

An fara boren ne da sanyin safiyar ranar Jumu'a a wani sansanin soji da ke birni Buoake na arewacin kasar.

An ji karar harbe-harbe a ranar Assabar a cikin wani sansanin soji da ke karshen birnin na Abijan daga gabas inda sojojin kundunbala na lema ke zama.

Sojojin sun toshe manyan hanyoyi kuma suna zagayawa a cikin motocin a kori kura suna harbi jefi-jefi.

Bazuwar boren zuwan Abijan dai manuniya ce ga cewa sojojin ba su ji dajin yadda gwamnati ta mayar da martani ga boren takwarorin nasu ba.

Shiga tsakani ta gamu da cikas

A halin yanzu an sako ministan tsaron kasar Alain-Richard Donwahi wanda sojojin suka tsare lokacin da ya je ganawa da wakilan masu bore.

Sun su suna so ne su gana da Shugaba Allasane Ouattara wanda ya yi tafiya zuwa kasar waje.

Sai dai shugaban kasar Ivory Coast, Alassane Ouattara ya ce ya cimma wata matsaya da za ta kawo karshen boren da sojojin ke yi.

Mr Ouattara ya ce za a yi nazari akan bukatun sojojin na neman karin albashi da kuma kyautata yanayin aiki,inda ya bukace su da su koma bariki a cigaba da aiki.

Sai dai sojojin ba su fito fili suka bayyana bukatun nasu ba.

Babu dai wani labarin samun rasa rai ko rauni kawo yanzu, amma dai mutane sun sha jinin jikinsu.

Wannan boren dai ya tunawa 'yan kasar da da rikicin siyasa da yakin basasar da kasar ta Ivory Coast ta yi fama da su tsawon shekaru goma, wanda ya kare a shekara ta 2011.