Hankali ya soma kwanciya a Ivory Coast bayan boren soji

An sake bude shaguna a birnin Bouake

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An sake bude shaguna a birnin Bouake

Sojoji sun daina boren da suka kwashe kwana biyu suna yi a kasar Ivory Coast inda suke bukatar a ba su alawus.

Mazauna Bouake da kuma masu aiko da rahotanni sun ce babu alamar tashin hankali a kan titunan birnin - kwana daya bayan soji sun kwace ma'aikatar tsaron kasar.

Boren ya bazu zuwa wurare da dama, ciki har da Abidjan, amma hankali ya kwanta a can ma.

A ranar Asabar ne aka sanya hannu a kan wata yarjejeniya tsakanin sojojin da suka yi bore da kuma gwamnati, sai dai babu cikakken bayani kan yarjejeniyar.

Waniwakilin kamfanin dillancin labarai na AFP a Bouake ya ce babu wani rahoton bude wuta a birnin tun ranar Asabar.