Buhari zai jagoranci tattaunawa kan Gambia

Asalin hoton, AFP
Muhammadu Buhari ya ce yana da kyakkyawan fata za a kawo karshen kiki-kakan na Gambia cikin ruwan sanyi
Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari zai karbi bakuncin wasu shugabanni 4 na kasashen yammacin Afrika domin tattaunawa kan dambarwar siyasar kasar Gambia, a ranar Litinin din nan.
Wata sanarwa daga fadar shugaban, ta ce, taron, ci gaban wata ganawa ce da shugabannin yammacin Afrikar suka yi a Accran Ghana, a lokacin rantsar da sabon shugaban kasar, Nana Akuffo-Addo a ranar Asabar.
Sanarwar ta ce shugaban zai jagoranci zaman ne domin lalubo hanyar da za a cimma masalaha a dambarwar da ta biyo bayan zaben Gambian.
Ce-ce-ku-cen ya samo asali ne dai bayan da Shugaba Yahya Jammeh, wanda da farko ya amsa shan kaye a zaben, ya dawo ya ce bai amince da faduwar ba.
Shugaban ya zargi kasashen waje da cewa su ne suka rikita zaben, abin da ya sa ya ce ya gabatar da korafinsa gaban kotun kolin kasar.
Shi kuwa a nasa bangaren jagoran 'yan hamayya Adama Baro, wanda aka ayyana ya ci zaben, ya lashi takobi cewa da zarar ranar 19 ga watan Janairu ta zo, zai tabbata shugaban kasar.