Jamus: Za a rika biyan nakasassu kudin lalata da karuwai

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gwamnatin Jamus ta halatta karuwanci a kasar tun 2002

Wata 'yar majalisr dokokin Jamus ta ce ya kamata gwamnati ta rika biyan nakasassu da masu tsananin rashin lafiya kudin lalata da karuwai.

Elisabeth Scharfenberg wadda ita ce mai magana da yawun jam'iyyar Green Party ta ce kafin a biya su kudaden lalatar sai sun bayar da shedar rashin lafiyar da kuma tabbatar da cewa ba su da karfin biyan kudin zuwa wurin karuwan.

A wata hira da 'yar majalisar ta yi da jaridar Welt am Sonntag ta Jamusanci ta ce, tana ganin lalle ya kamata gwamnati ta rika ba da wannan tallafi na lalata ga wannan rukuni na mabukata.

Jaridar a sharhin da ta rubuta, ta ce, ana samun karin karuwai da suke zuwa gidajen kula da nakasassu da sauran majiyyata domin biya musu bukata.

Wani kwararre mai bayar da shawara kan jima'i, a gidajen kula da majiyyata da nakasassu, ya gaya wa jaridar cewa, karuwai alheri ne ga wasu marassa lafiyar.

A kasar Holland mutum yana da damar neman gwamnati ta biya shi kudin da ya kashe ya yi lalata da karuwa, a matsayin hakkinsa na magani ko kula da lafiya.

Jam'iyyar Green Party wadda ta fi girma a Jamus fiye da a kowace kasa, ta yi nasarar shiga gwamnatin hadaka a Jamus, karon farko a 2011.