Nigeria: Shugabanni sun kammala tattaunawa kan rikicin Gambia

Najeriya ECOWAS

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

ECOWAS na tattaunawa kan rikicin Gambia

Tawagar Ecowas zata kai ziyara Gambia ranar Laraba su kara matsawa Yahya Jammeh ya mika mulki ga Adama Barrow.

An dauki wannan mataki ne bayan wata ganawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi da wasu shugabannin kasashen yammacin Afirka guda hudu a Abuja, babban birnin kasar.

A ranar litini ne dai shugabannin kasashen yammacin Afirka suka yi ganawar domin warware rikicin siyasar kasar Gambia.

Daga cikin shugabannin da suka halarci taron, wanda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jagoranta, har da Ellen Johnson Sirleaf ta Liberia, da kuma tsohon shugaban kasar Ghana John Mahama wanda ya mika mulki a shekaranjiya Asabar.

Shugaban Gambia, Yahya Jammeh dai ya ki amincewa da mika mulki bayan an kada shi a zabe cikin watan jiya.

Hukumomin kasar sun rufe gidan rediyo na 4 a jiya Lahadi, inda ma'aikatan Paradise FM suka ce 'yan sanda sun umarce su, su dakatar da yada shirye-shirye.

Ba su bayar da wani dalili kan daukar wannan mataki ba.