China ta gargadi Amurka kan ziyarar shugaban Taiwan

Tsai Ing-wen

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Dalilin da ya sa Beijing ta mai da hankali akan tafiyar Tsai Ing-wen zuwa Amurka

Kafofin watsa labarai a China sun ce kasar ta gargadi Amurka kan karkacẽwa daga manufofin China kasar daya ce, sa'o'i bayan da shugaban Taiwan ta kai ziyara a Houston.

Shugaba Tsai Ing-wen ta samu hira da dan majalisar dattiwan Texas, Ted Cruz da Gwamna Greg Abbott a lokacin da ta tsaya akan hanya zuwa Amurka ta tsakiya.

Kakakin shugaban kasa mai jiran gado Donald Trump ta ce a ranar Asabar shugaba Donald Trump ko tawagar sa ba za su hadu da Ms Tsai ba.

China ta mayar da martani da fushi a lokacin da Mr Trump ya yi hira da Ms Tsai ta wayar tarho karshen shekaran da ta wuce.

Ba wani shugaban Amurka ko kuwa shugaba mai jiran gado da ya taba hira da shugaban Taiwan kai tsaye a shekaru da dama.

Wata jarida a kasar ta ce, ba wajibi ba ne Beijing ta yiwa Mr trump godiya domin ba zai hadu da Ms Tsai, saboda manufofi na China kasa daya ne, ita ce tushen dangantakar China da Amurka.

Bin wannan ka'ida ba hukunci da China ke bukata daga shugabannin Amurka ba ne, amma wani wajibi ne akan shugabannin Amurka su tabbatar da dangantakar da ke tsakanin China da Amurka.

Ba bu damar wata tattaunawa akan lamarin.