Tsohon shugaban Chadi Hissene Habre ya nemi a soke hukuncin kotu

Hissene Habre

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Hissene Habre be amince da yake hukuncin da aka yi masa ba

Tsohon shugaban kasar Chadi, Hissene Habre ya tafi kotu don neman a soke hukuncin da aka yanke masa a bisa aikata laifuka kan bil'adama.

Lauyoyin sa sun bayana cewa kasar Senegal da kungiyar tarayyar Afrika suka shirya wannan gwaji ta musamman wanda a ganin su ke da wasu kura-kurai.

Sun kuma ce ba a mutunta 'yancin wanda ake tuhuma ba.

Mr Habre shi ne tsohon shugaba kasa na farko da kotun kungiyar tarayyar Afrika ta yi wa shari'a.

Asalin hoton, ANDREW STOEHLEIN/HRW

Bayanan hoto,

Hukuncin da aka yi wa Hissene Habre a watan Mayun bara ya sa ana murma a cikin kotun

Shari'ar dai na da muhimmacin ga daukacin nahiyar Afrika.

Tsohon shugaban ya mulki kasar Chadi daga shekarar 1982 zuwa 1990, lokacin da aka kifar da mulki sa.

Bayyan hakan ne ya yi gudun hijira zuwa Dakar, babban birnin kasar Senegal.

An yanke masa hukunci daurin rai da rai kan laifukan aikata fyade, da kuma bada umarnin kashe-kashe da dama.

Mr Habre ya ce wannan kotu ta musamman ba ta da wani iko a kan shi kuma ba zai zo a bainar jama'a ba.

Idan kotu mara baya wa hukuncin, zai cigaba da kasancewa a kasar Senegal ko kuma a wata kasa dake cikin kungiyar tarayyar Afirka.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Hissene Habre ya ki amincewa da halalcin kotun da ta yi shari'ar shi