Kenya na fama da matsanancin rashin wuta

Wani mai gayaran wuta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan kasuwa sun bukaci gwamnati ta shawo kan matsalar saboda yana shafar kasuwancinsu

Wurare daban-daban na fama da matsanancin rashin wutar lantarki a kasar Kenya tun a yammacin ranar Lahadi.

Matsalar ta afku ne bayan an samu matsalar na'ura a daya daga cikin tashoshin samar da wutar lantarkin.

A samu abkuwar makamancin hakan a bara inda kamfanin wutar lantarki na Kenya ya dora alhakin a kan wani biri.

Nairobi babban birnin Kenya da kuma yankunan dake bakin teku da lardunan dake arewacin kasar ne ke fuskantar rashin wutar.

Kamfanin wutar lantarki na Kenya Power ya ce yana kokari domin shawo kan matsalar.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce " an samu matsalar na'ura ne a wani bangare na tashar wutar lantarki da ke Nairobi da safe wanda ya jawo rashin wuta daga birnin Olkaria da yankunan da ke bakin ruwa da kuma lardunan da ke Mt. Kenya.

Rashin wutar ya shafi garin Thika da ke dauke da masana'antun Kenya da dama dake lardin tsakiyar kasar.

Lamarin ya faru ne a lokacin da shugaba Uhuru Kenyata ke wata ganawa a ranar Lahadi, abin da ya haifar fargaba sai dai daga bisani an samar da wutar ta wata hanyar kuma aka cigaba da ganawar.