An gano mutum 16 a fashin da aka yiwa Kardashian a Paris

Kim Kardashian West

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kim Kardashian ta ce ta tsorata saboda ta zaci 'yan fashin za su kashe ta a lokacin fashin

'Yan sandan Faransa sun tsare mutum 16 saboda alakarsu da fashin da aka yi wa mashahuriyar mai fitowa a shirye-shiryen talbijin a Amurka, Kim Kardashian.

An kama mutanen a yankin birnin Paris da sauran yankunan kasar guda biyu.

Matakin dai ya biyo bayan binciken wata uku da aka yi kan fashin, bayan wasu dauke da makamai sun fasa gidan tauraruwar a birnin Paris cikin watan Oktoban bara.

Yan fashin sunyi awon gaba da kudi dala miliyan 9 da rabi da kuma gwala-gwalanta.

'Yan sanda sun ce an bi sawun mutanen da ake zargi ne bayan an gano zanen halittun fayyace Dan'adam a wajen.