'Za mu 'yanto kananan hukumomi daga jihohi'

Sanata Bukola Saraki, tsohon gwamnan jihar Kwara ne

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, tsohon gwamna ne, wadanda suka assasa zaman kananan hukumomi karkashin jiha

Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan Najeriya Sanata Ali Ndume ya ce, a zaman da za su ci gaba da yi bayan dawowa daga hutun karshen shekara, za su mayar da hankali wajen 'yanto kananan hukumomi daga jihohi.

A ranar Talatar nan ne `yan majalisar dokokin Najeriyar za su koma bakin aiki, bayan hutun, inda za su ci gaba da tattaunawa kan wasu muhimman batutuwa na kasar.

Daga cikin abubuwan da za su ci gaba da tattaunawar akwai batun duba kasafin kudin 2017 wanda shugaban kasar ya mika wa majalisun kafin tafiya hutun.

Akwai kuma batun tantance shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta`annati EFCC, Ibrahim Magu, wanda ke gaban majalisar dattawa.

A hirarsa da BBC, shugaban masu rinjayen, ya ce za su mayar da hankali wajen gyaran kundin tsarin mulkin kasar ta yadda kananan hukumomi za su samu 'yancinsu daga gwamnatocin jihohi.

Ya ce tsarin da ake da shi yanzu inda gwamnatocin jihohi ke iko da kananan hukumomi, yana tauye ci gaban al'umma kasancewar kananan hukumomin sun fi kusanci da jama'a.

Sanata Ndume ya kuma ce za su ci gaba da tattauna batun amincewa da nadin Ibrahim Magun a matsayin shugaban EFCC, idan fadar shugaban kasar ta sake kawo musu bayani kansa.

Kafin tafiyarsu hutu 'yan majalisar sun yi watsi da batun tabbatar wa Ibrahim Magun shugabancin hukumar ta EFCC, bisa bayanai biyu masu karo da juna da hukumar tsaro ta farin kaya ta SSS ta bayar a kansa.

Bayani daya na zarginsa da almundahana, dayan kuma na tabbatar da dattakunsa.